Gwamnatin jihar Kwara ta fara rushe gidan Olusola Saraki a birnin Illorin. Da misalin karfe 4 na asuba ranar Alhamis ne aka fara rushe ginin. Wannan ya faru ne bayan jami'an tsaro sun tarwatsa wasu matasa da suka ja daga suna turjewa domin hana rushe ginin.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, tun ranar Laraba da karfe 2 na dare Gwamnatin jihar Kwara ta yi yunkurin rushe ginin, amma wadannan matasa suka turje, lamari da ya hana gudanar da aikin rushe ginin.
Wannan gini da aka fi sani da Ile Arugbo, an rushe shi da karfe 4 na asuba. Tun 1999, iyalin Olusola Saraki ke juya akalar siyasar jihar Kwara, wanda haka ya samar da Bukola Saraki dan Olusola Saraki a matsayin Gwamnan jihar Kwara, kuma daga bisani ya zama shugaban majalisar Dattawan Najeriya a 2015 zuwa 2019, hakazalika gidan ya samaar da manyan yan siyasa da suka rike kujerin siyasa.
Gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazak, ya sanar da sanarwar kwace wannan fili yana mai cewa an mallaki filin ne ba bisa ka'ida ba.
Amma Bukola Saraki ya ce Gwamnatin jihar Kwara tana yi masa bita da kulli ne saboda manufa ta siyasa, ya ce an mallaki filin bisa ka'ida.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari