Rundunar yansandan jihar Abia ta cafke wasu yan fashi da makami yan kungiyar kusurgumin dan fashi da yansandan jihar suka bindige har lahari mai suna Theukwumere
Nwokochada, wanda aka fi sani da suna "Grave" kamar yadda Talaabijin na ABN TV ta labarta.

Kwamishinan yansandan jihar Abia, CP. Etim Ene Okon, ya ce yayin da jama'a a birnin Umuahia suke farin ciki kan kisan "Grave" domin fashi da makami ya ragu a birnin. Sai wasu magoya bayansa suka bullo suka addabi birnin Umuahia, kuma hakan ya sa yansanda farautarsu har suka cafke su da ransu.
Sai dai abin mamaki shine yadda aka gan wani hoton gawakin yan fashin da aka kama. Babu wani rahotun cewa an gurfanar da wadanda yan fashin a gaban Kotu kafin mutuwarsu ko rahotum kan musabbabin mutuwarsu.
DAGA
ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari