• Labaran yau


  Hotunan dakin taro na Lugard mai shekara 106 da ginawa a birnin Kaduna

  Dakin taro na Lugard an gina shi a tsakiyar kewayayyen hanya wanda ke arewacin birnin Kaduna. Yana makwabta da Murtala square daga arewa, kuma ginin yana da tsarin salon gini irin na Sarakunan arewa tare da ado a farfajiyar ginin wanda ke tsaye a fuskar ainihin unguwar.

  Gwamnatin mulkin mallaka na Turawan Ingila ne suka gina shi a shekararar 1914, an yi wannan gini ne sakamakon dauke shelkwatar arewacin Najeriya daga garin Zungeru zuwa garin Kaduna a 1911.

  Tsohon Gwamnan arewacin Najeriya Lord Lugard ne ya kawo tsarin ginin daga kasar Indiya a lokacin da ya zama Gwamnan arewacin Najeriya a 1904.

  DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

  https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

   Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Hotunan dakin taro na Lugard mai shekara 106 da ginawa a birnin Kaduna Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama