Bidiyon batsa a arewa: Daya daga cikin 'yammatan faifain bidiyon ta kashe kanta

Rahotun Legit Hausa

Tashin hankali da tashin-tashina sun barke bayan wani mutum mai suna Emeka ya saki wasu bidiyo na batsa da ya nada na wasu 'yan mata da matan aure da ke Jos, jihar Filato. An gano cewa mutumin na zama ne a yankin Rayfield da ke Jos.

An zarge shi da ba wa matan dubu talatin-talatin sannan yayi lalata dasu tare da nadar bidiyon. Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, tuni bidiyon wannan abu ya yawaita a jihar. Daya daga cikin matan da aka yi bidiyon da ita kuwa ta kashe kanta bayan yaduwar shi.




Rahoton ya bayyana cewa Emeka yayi wa matan alkawarin biyansu N100,000 duk shekara. Daya daga cikin matan wacce tayi hira da jaridar Daily Trust kuma ta bukaci a boye sunanta ta ce wata mata ce ta sameta a wajen shakatawa a kan cewa suna bukatar mata masu irin surarta don fitowa a wani fim kuma za a biya su sosai.

Majiyar wacce ta tabbatar da mutuwar daya daga cikin wadanda abin ya faru da ita, tace sun je tare da kawarta wajen kuma aka karbesu tare. "Matar da ta kaimu an bata naira dubu ashirin saboda kaimu da tayi.

Na jira a wani daki tare da matar a lokacin da kawata suke yi da Emeka kuma ana nadar bidiyon kafin a zo kaina. "Daga nan sai muka kwana a otal din saboda dare yayi amma da safe kowa ya watse," in ji ta. Ta kara da cewa lamarin ya faru ne kusan shekara daya da ta gabata kuma Emeka ya yi alkawarin biyansu dubu dari duk shekara.




Hakazalika ya bukaci su cigaba da kawo 'yan mata don wannan harkar. Budurwar ta ce tun bayan sakin bidiyon, ta fara samun matsaloli da 'yan uwanta kuma saurayinta na gudunta.

A yayin mayar da martani a kan aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Tyopev Terna ya ce rundunar ta ji jita-jitar al'amarin amma babu wanda ya garzayo don kawo musu rahoto.

Ya yi kira ga wadanda abin ya shafa da kada su ji kunya ko tsoro, su garzayo don kawo kokensu don a bincika tare da daukan matakin da ya dace. n-bidiyon-ta-kashe-kanta.html

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN