Rahotun Legit Hausa
A lokutan baya mace kan zama abin nunawa a idon duniya, idan
har ta kai wani shekaru bata yi aure ba. Abin ma har ya kan shafi zaurawa mata
da matan da suka ki aure bayan mazajen su suka rasu.
Sai dai a zamanin nan da muke ciki abun ya sha bamban, domin
sai ka ga mace ta girma har wuci aure amma tana gaban iyayenta saboda wasu
dalilai wanda mafi akasarinsu ba kwarara bane.
Ga wasu daga cikin dalilan da
ake ganin suna hana matan arewa aure a wannan zamanin:
1. Kwadayi da son abin duniya: A wannan zamani da muke ciki,
mata da dama sun daukar wa kansu dala ba ganmo, inda son jin dadi da watayawa
kan sa zaman aure ya gagare wasu da yawa. Wasu matan kan so a yi ta jin dadi
ne. Idan miji ya samu kararyar arziki shike nan sai ta yi ta dabalbale sa da
fitina. Nayau dabam da na gobe. duk don ta samu damar sheke ayar ta a waje ta
yi abin da taga dama.
2. Daidaita jinsin Mace da Namiji: Yanzu akwai kungiyoyi da
suka fito suna kira ga mata da su nemi hakkin su a wajen mazajen su. Cewa
daidai suke da maza. Idan Ta goya yaro shima gobe ya goya yaron Sannan ma su
raba ranakun girki da wanke- wanke. Duka irin haka na dada rudin mata wajenkin zaman
aure.
3. Yaudara: Wasu matan kan fada tarkon mazaje masu yaudara.
Idan har mace bata yi sa’an samun nagari ba sai kaga ta fada cikin irin wannan
hali da hakan sai ya sa ayi ta fama da ita. Taki yi auren ko kuma ma sauraren
wani namiji.
4. Nuna Isa: Kamar yadda suka bayyana. Mata a wannan zamani
suna son ace suma sai yadda suke so za ayi. Hakan yasa wasu da dama basu iya
zama karkashin wani namiji da sunan wai a karkashin shi suke. Idan tana zamn
kanta to zata yi abinda da take so babu mai takura mata.
5. Tsananin talauci da Dogon Buri: Wannan shima babban
matsala ce da ake fana da shi a wannan zamani da muke ciki. Rashin abin hannu
da kuma cika tumbi da aka yi da burin tsiya kan sa mata su ki yin auren
kwata-kwata ko kuma ma da sun yi su ki zama.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Domin zama wakilinmu a garinku LATASA NAN KA TUNTUBE MU