Bagudu ya sa sabbin sakatarorin ilimin framare 21 rantsuwa a jihar Kebbi

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, ya rantsar da sabin Sakatarorin ilimi ES, na kananan hukumomi 21 da ke jihar Kebbi ranar Laraba 29 ga watan Janairu, a dakin taro na shugaban kasa da ke garin Birnin kebbi.

Mai ba Gwamnan jihar Kebbi shawara kan harkar yada labarai Yahaya Sarki, ya sa hannu a wata takardar bayan taro dauke da sanarwar rantsarwar.

Wadanda aka rantsar kwararru ne kan harkar ilimi, Manyan Malaman Jami'oi, kuma an zakulo su ne domin a tabbatar da ganin cewa an yi nassara a tsarin ilimin bai daya na Gwamnati watau Basic Education for All (BESDA) a kananan hukumomi 21 da ke jihar.

Wadanda aka rantsar su ne:

1) Aliero - Prof Ibrahim Hussaini
2) Arewa - Dr. Muhammed Aminu Bui
3) Argungu - Prof Rabi Muhammed
4) Augie - Prof Muhd Aminu Bayawa
5) Bagudo - Prof Ibrahim Muhd Bandi Zagga
6) Birnin Kebbi - Prof Umar Aliyu Chika
7) Bunza - Prof- Aliyu Muhd Bunza
8) Dandi - Dr.Samaila Kamba
9) Danko Wasagu - Dr.Nasir Muhd Baba
10) Fakai - Prof Muhd Garba Mahuta
11) Gwandu - Prof Muhd Shalla Bello
12) Jega - Prof Suleiman Khalid
13) Kalgo - Prof Faruku Aliyu Kalgo
14) Koko /Besse - Prof Abubakar Dan Baba
15) Maiyama - Dr.Balarabe Isah Adamu
16) Ngaski - Prof. Umar Abubakar B/ Yauri
17) Sakaba - Prof Sanusi Muhd
18) Shanga - Dr.Abdulbasit Ahmed Atuwo
19) Suru - Dr. Sodangi Umar
20) Yauri - Prof.Sadiq  Abdullahi Yelwa
21) Zuru - Dr. Sani  Dantani Manga 

Hotuna: Anas Hoja

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN