Zargin kisan wata budurwa a garin Birnin kebbi, yansandan jihar Kebbi na bincike

Rundunar yansandan jihar Kebbi tana bincike kan musabbabin mutuwar wata yarinya mai suna Hauwa ranar Juma'a 29 ga watan Nuwanba, bayan an gano gawarta a unguwar bayan Sakatariyar Haliru Abdu da ke garin Birnin kebbi bayan Sallar La'asar.

Mujallar ISYAKU.COM ya samo cewa har yanzu ba'a gane wadanda suka kashe ko musabbabin mutuwar Hauwa ba, wacce yar asalin unguwar 'Yar yara ne a garin Birnin kebbi. Sai dai Kakakin hukumar yansandan jihar Kebbi, DSP Nafi'u Abubakar ya tabbatar da mutuwar wata mace da aka samo gawarta a unguwar bayan Haliru Abdu kuma yansanda sun dukufa wajen bincike kan lamarin.

A gefen gawar Hauwa, an ga Hijabinta mai ruwan toka, da kwalfar wayoyinta na salula amma babu wayoyin a ciki, da wani gashin kai na mata kamar yadda ya bayyana a hoton gawarta.

Unguwar bayan Sakatariyar Haliru Abdu, na daya daga cikin unguwanni da babu yawan hada hada da kai kawo na jama'a, ko da tsakiyar rana sakamakon yanayi na zamantakewa.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post