Zaben 2023: Ekweremadu, Goje, da Gwamna Masari za su ajiye kambu

Rahotun jaridar Legit Hausa

Mun tattaro maku jerin wasu gawurtattun ‘Yan siyasan Najeriya da su ke shirin rabuwa da takara daga zabe mai zuwa. Wannan jeri ya na kunshe da Sanatoci biyu da kuma gwamna mai-ci wanda su ka fito daga jam’iyyun PDP da kuma APC.

1. Ike Ekweremadu Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, ya sanar da Duniya cewa ba zai sake neman takara a 2023 bayan shekaru fiye da 20 ya na bugawa. A cewarsa ya samu damar yi wa jama’ansa duk wata hidima a mukaman da ya samu kansa. Ekweremadu ya bayyana wannan ne lokacin da ya cika shekaru 57.

2. Mohammed Danjuma Goje Sanata Mohammed Danjuma Goje wanda ke wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa ya shaidawa mutanensa cewa babu shi babu maganar tazarce a 2023 A wajen wani taro da aka yi a filin wasa da ke Pantami a jihar Gombe, tsohon gwamna ya ce zai bar wa Matasa takara bayan ya rike kujerar Minista da Majalisa.

3. Aminu Bello Masari Mai girma Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya nuna cewa ya na cikin wadanda ba za a sake ganin sunansu a jeringiyar ‘Yan takarar siyasa daga yanzu ba. Aminu Masari wanda ya taba rike kujerar shugaban majalisar wakilan tarayya ya tabbatarwa mutane a Katsina cewa zai ajiye siyasa ganin shekarunsa sun ja.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN