Yansandan jihar Kebbi sun kama barayin motoci daga kasar Nijar da masu aikata manyan laifuka

Rundunar yansandan jihar Kebbi ta yi nassarar kama wasu bata gari da dama, wadanda suka hada da yan fashi da makami, masu satar mutane domin karbar kudin fansa, wadanda suka aikata kisan kai, da sauran laifuka a zango wata uku na karshen shekara ta 2019.

Yayin da yake jawabi wa manema labarai a ofishinsa da ke shelkwatan yansanda a garin Birnin kebbi, Kwamishinan yansanda jihar Kebbi Garba M.D, ya ce :

" Domin tabbatar da an yi bukukuwan karshen shekara lafiya kalau a jihar Kebbi, ina son in jaddada cewa dokar hana amfani da ababen bukukuwa masu fashewa kamar su fireworks, fire crackers, bangers, knockouts da sauran ababen shagulgula masu fashewa ko tartsatsin wuta, tana nan daram.
Sakamakon haka muna shawartar iyayen yara su sa ido domin ganin cewa ba a sami bacewar yara ba a lokacin bukukuwan".

Hakazalika, Kwamishinan ya yi kira ga jama'ar jihar Kebbi, cewa su kai rahotun duk wanda suke tababa ko basu amince da halayensa ba a cikin al'u,ma ga yansanda. Ya ce:

" Ina kira ga mutanen jihar Kebbi masu bin doka, cewa su sa ido a kan ababen da ke zuwa suna komowa a cikinsu, kuma su kai rahotu ga yansanda ko wasu jami'an tsaro a kan mutumin da basu yadda da take-takensa ba a cin al'umma".

Rundunar ta kama wani Ibrahim Usman Yusuf daga Sabon garin Arawa a karamar hukumar Kebbe da ke jihar Sokoto bisa tuhumar cewa shi ne ke kai wa masu satara mutane abinci da suka addabi jama'a a yankin Maiyama, Koko da Bagudo.

Hakazalika rundunar ta kama Aliyu Garba da Aliyu Barde daga Rafin Kirya da ke karamar hukumar Shanga, bayan sun sace Usman Usman ranar 14 ga watan Oktoba, suka kai shi wani waje da misalin karfe 1:30 na dare. Daga bisani Usman ya gane su kuma ya kai rahotu wajen yansanda, kuma aka cafke su.

An kama wani kabila mai suna Gabriel Egbuke daga kauyen Maizaga a karamar hukumar Bagudo, bayan sun yi wa Alhaji Muhammadu Janyo fashi suka karbi N70.000, kuma suka nemi kudin fansa Naira miliyan 2 wai idan ba haka ba za su kashe shi. Bayan yansanda sun sami rahotu, an kama Gebriel yayin da sauran biyu suka tsere.

Kwamishinan ya kara da cewa " Ranar 26 ga watan Oktoba, da misalin karfe 2 na dare, wasu barayi sun shiga gidan Abu Hali da ke unguwar Gesse 2 a garin Birnin kebbi, suka sace masa mota kirar Landcruiser Jeep da wayayin salula guda 2. Haka zalika gungun wadanda suka aikata wannan laifi sun je gidan Shehu Umar ranar 3 ga watan Nuwamba da misalin karfe 3:30 na Asuba a unguwar Bye pass a garin Birnin kebbi, suka sace motocinsa guda biyu, Toyota Camry 2013 da Camry 2014, sun kuma sace Dalan Amurka 2000.

Bayan yansanda sun sami rahotu, masu bincike na yansanda sun shiga bincike kuma suka yi nassarar kama Abubakar Muhammad daga garin Tawa a jamhuriyar Niger, Muh'd Auwal daga jihar Kano, Yahaya Bilal daga Birnin kebbi jihar Kebbi, da Salahu Makada daga Argungu a jihar Kebbi. Wadanda aka kama sun shaida wa yansanda cewa sun aikata laifin, sun kuma ce madugun gungun nasu Abdullahi Musa dan garin Illela ne a jihar Sokoto, Mustapha Abubakar da Muhammed Rabi'u duk yan jihar Kano ne kuma sun tsere yayin da ake ci gaba da bincike domin ganin an kamo wadanda suka tsere.

Kwamishina Garba M.D ya bukaci al'umman jihar Kebbi su ci gaba da bin doka da oda, tare da kai rahotun abin da basu lamunta da shi ba a bangaren tsaro domin inganta zaman lafiya a cikin al'umman jihar Kebbi.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN