Yan daban siyasa sun yi kokarin cin zarafin Hadiza Bala Usman a Majalisan Dattawa

Legit Hausa

Hadiza Bala Usman, manajan daraktan hukumar jiragen ruwa ta Najeriya,
ta yi kira da cewa a binciki wasu mutane da take zargi da hantararta a
farfajiyar majalisar dattijai.

A koken da ta mika ga sifeta janar din 'yan sanda, shugaban majalisar dattijai da kuma shugaban hukumar jami'an tsaro na fararen kaya, Usman ta yi bayanin zuwan da ta yi
majalisar don amsa gayyatar da aka yi mata a majalisar.

Ta bayyana cewa, wasu mutane sun hareta wadanda take zargin hayarsu aka yi. Ta
zargi Idahosa Okunbo, shugaban OMSL da wannan lamarin. "A yayin taron,
Kaftin Idahosa na OMSL, bayan ya yi bayaninsa, ya fita daga taron a
harzuke kuma da matukar fushi," ta bayyana a kokenta.

Ta ce, "Bayan fitarsa, sai shugaban kwamitin hadin guiwar da ya gayyacemu majalisar
ya rufe taron. Bayan fita daga dakin taron, wasu 'yan daba da suka
rako Kaftin Idahosa sun biyoni har kofar fita kuma sun yi kokarin su
tarar dani gaba da gaba.

Sun zazzageni cewa ina toshe musu da ubangidansu hanyar cin abinci kuma zasu nemoni tare da tarwatsani." Ta kara da cewa, kokarin jami'an tsaron da take tare da su ne tare da
jami'an tsaron ofishin mataimakin shugaban majalisar dattijai ne ta
samu fita tare da tawagarta ba tare da sun cimma burinsu ba. Ta ce
yakamata a tuhumi Okunbo matukar wani abu mummuna ya faru da ita ko
wani iyalinta.
Previous Post Next Post