Yadda wani magidanci ya kashe dansa da hannunsa a jihar Kano

Legit Hausa

Jami'an hukumar 'yansan jihar Kano sun samu nasarar kama wani mutumi
magidanci, inda suke tuhumar sa da kashe dansa na cikinsa mai kimanin
shekaru uku.

Mutumin da aka bayyana sunanshi da Musbahu, wanda yake
zaune a unguwar mahaukaci dake karamar hukumar Gaya cikin jihar Kano,
ya sanyawa dan nasa shinkafar bera a cikin abinci, inda yaron na ci
yace ga garinku nan.

A hirar da mutumin yayi da wakilin freedom rediyo
dake Kano, magidancin ya bayyana cewa yayi wannan aika-aika ne saboda
dan nashin ba ta hanyar aure ya same shi ba, sannan kuma babu wata
wacce za ta rike masa yaron, wannan dalilin ne yasa ya sanya masa guba
a cikin abinci ya ci ya mutu.

Sai dai kuma magidancin ya nemi ayi masa
sassauci akan laifin da ya aikata. Mai magana da yawun rundunar 'yan
sandan ta jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa da
sun kammala binciken su akan wannan magidanci za su mika shi gaban
kuliya domin ya fuskanci hukunci daidai da abinda ya aikata.

Wannan dai ba shine karo na farko da irin haka take faruwa a Najeriya ba, sau
da dama an sha kama uba ya kashe danshi ko kuma da ya kashe
mahaifinshi.
Previous Post Next Post