Yadda wani dansanda ya yi wa matarsa duka jina-jina saboda N500 a Kaduna

Fitaccen Jaridar Husa wanda ake wallafawa a shafin yanar gizo watau Legit Hausa ta ruwaito cewa wata mata wacce har yanzu ba a gano sunanta ba ta jawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani sakamakon hotunanta face-face cikin jini da ke yawo.

Kamar yadda ake zargi, mijin matar dan sanda ne ma’aikaci a jihar Kaduna. Dan sandan ya yi wa matarshi mugun duka ne a kan dan hargitsi da suka samu akan naira dari biyar. Mijin da aka gano sunansa da Sajan Yusuf Bello yayi wa matarshi jina-jina ne bayan da suka yi fada a kan wannan kudin.

A yayin mayar da martani a kan wannan cigaban, kwamishinar walwalar jama’a ta jihar Kaduna, Hafsat Baba ta wallafa wannan labarin a yanar gizo. Ta yi alkawarin gano jami’in dan sandan tare da ladabtar da shi.Kamar yadda kwamishinar ta wallafa a shafinta na tuwita, “na lura cewa wannan lamarin ya fara yawaita. Jami’an tsaro na jin kamar sun fi karfin hukuma.

Ina kira ga hukumar ‘yan sandan Najeriya da sauran jami’an tsaron da abun ya shafa, da su dauki matakin gaggawa.“Mun kai koken mu ga ma’aikatar tsaron cikin gida a karkashin Samuel Aruwan. Muna da tabbacin za a dau mataki a kan wannan lamarin.

Amma kuma, akwai bukatar mu tattauna a kan daililin wannan cin zarafin da mata ke fuskanta a gidajen aurensu.“Abun na cin min tuwo a kwarya ta yadda wannan mijin ya yi wa matarshi. Wannan Sajan Yusuf Bello din ya yi wa matar shi duka ne a kan N500.

Ina soyayya da mutunta junan dake tsakanin mata da miji suka tafi?”

Source: https://hausa.legit.ng/1287159-hotuna-dan-sanda-ya-yiwa-matarsa-dukan-kawo-wuka-kan-n500-a-kaduna.html

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN