Yadda tsofaffin mata fiye da 100 suka yi zanga-zanga tsirara a wata jihar kudu | ISYAKU.COM

Kimanin mata 100 masu shekara 50 zuwa 80 sun gudanar da wani tattaki tsirara a jihar Ebonyi sakamakon kama yayansu da jami'an tsaro suka yi a jihar. Wadannan mata sun fito daga garin Agubia na karamar hukumar Ikwo a jihar ta Ebonyi.

Matan sun yi cincirindo a kofar shiga gidan gwamnatin jihar da misalin karfe 11:00 na safe ranar Litinin, suna bukatar a gaggauta sakin yayansu da jami'an tsaro suka kama bayan aukuwan wani riki a garin Agbia Ikwo yan kwanakin baya.Matan sun je da niyyar ganin Gwamnan jihar Ebonyi, amma ba a bari suka yi ido biyu da shi ba a gidan gwamnati da ke Abakiliki.

Mujallar ISYAKU.COM  ya samo cewa an sami barkewar wani rikici ne mako hudu da suka gabata a garin Agubia tsakanin wasu kungiyoyi biyu kan ko waye zai mallaki wani tashar mota, lamari da ya kai ga salwantar rayuka da dukiyoyin miliyoyin naira.

Mrs Mercy Nwali, wacce ta yi jawabia amadadin sauran matan ta ce sun je gidan gwamnati ne domin neman a sasanta kuma a saki yayansu da aka kama. Ta ce kama yayansu da aka yi ya jefa iyalansu cikin matukar damuwa.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post