Yadda sabuwar wakar kalubalen siyasa na mawakan jihar Kebbi ya tayar da kura | ISYAKU.COM

Fitowar wata waka daga mawakan jihar Kebbi ranar Asabar 7 ga watan Disamba 2019 ya zama abin zantawa a bayan fage na shafukan sada zumunta da zaurukan Whatsapp kasancewa wakar an yi ta ne a dunkule duk da yake ba'a ambaci sunan kowa ba. Amma sun alakanta wakar ne ga wani babban dan siyasa.

Amma wannan waka tuni ta zagaya kamar wutan dare a jihar Kebbi, Mujallar ISYAKU.COM ya tattaro cewa dubu dubatan mutane suka yi ta neman wannan waka ruwa jallo, amma yunkurin mu na samun wakar a wajen masu saka waka a gefen titi ya gagara.

Sai dai mun ci karo da wani matashi bayan Sallar Magariba ranar Asarbar wanda muka ji yana sauraron wannan waka a titin Akmadu Bello a wayarsa ta Android inda muka bukaci ya tura mana ta Xender.

Yanzu haka, wani bincike da muka gudanar ya tabbatar cewa wasu yan siyasa a jihar Kebbi sun nemi gaban mawaka da suka rera wakar domin yin sulhu, kasancewa wadannan mawaka sune suka yi ta yi ma yan siyasar jihar Kebbi wakoki kafin zaben 2015.

Sai dai ko da an yi sulhu, mun lura cewa wannan wakar ta riga ta illata siyasar wasu yan siyasa da babu salo ko sabulu da zai sake tsabtace yanayin siyasarsu.

Haka zalika, Mujallar ISYAKU.COM ya samo daga daya daga cikin Mawakan cewa " Malam Isyaku, wannan waka soma tabi ne kawai, wallahi akwai abubuwa da suka fi wannan kuma sai mun fallasa su".

Ana cikin haka ne, kwatsam sai ga wasu matasa mawaka a jihar Kebbi sun fitar da waka da suka rattaba wa suna " RADDIN MATASAN MAWAKA". A cikin wakarsu, sun kalubalanci mawakan farko, bisa da'awar da suka yi a cikin wakarsu da suka yi da farko.

Ko miye ke faruwa da ya haifar da wannan lamari, bisa dukkan alamu mutunci na neman subule wa wasu yan siyasa, ta yadda tasirinsu nan gaba a siyasance zai zama wani abin shakka a fuskan talakawan jihar Kebbi da wakar Mawakan ya sa suka farga bisa ababe da aka dade ana zargin wasu yan siyasa da aikatawa a fagen shugabanci da siyasan jihar Kebbi.

1 - Saurari sautin kalubale ga wani dan siyasa:

Latsa nan ka sauke sautin kalubale

2 - Saurari sautin radi kan wakar farko:

Latsa nan ka sauke sautin raddi kan waakar farko


DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post