Yadda kani ya jagoranci sace 'dan yayansa, ya karbi N300.000 kuma ya kashe yaron

Legit Hausa

Faruq Seidu mutum ne mai shekaru 34 a duniya wanda ake zargi da daukar kwangilar wasu mutane uku da suka sace yaron dan uwansa mai suna Abdulmalik Musa. Bayan sace yaron, sun karba kudin fansa har N300,000 inda daga bisani suka kashe yaron har lahira.

An gano cewa, an sace mamacin ne a ranar Larabar da ta gabata a gidan iyayensa da ke Sabo Ilupeju, Abeokuta a jihar ogun. Sun yi hakan ne da hadin bakin Seidu. Seidu da sauran wadanda ake zargin da garkuwa da yaron, an cafkesu ne a ranar Litinin a inda suka aikata kisan, kusa da kogin Ogun da ke Lafenwa a Abeokuta.

An zargi cewa, a nan ne masu garkuwa da mutanen suka shakesa har lahira. Wadanda ake zargin sun jagoranci jami’an ‘yan sanda bayan an cafkesu, zuwa inda gawar yaron take. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi, ya kwatanta wannan abu da suka aikata da rashin tausayin dan Adam.

Ya ce, bincike ya bayyana cewa, Seidu ya dau kwangilar abokansa uku ne saboda mahaifin yaron ya hanashi kudin karo mata ta uku. Oyeyemi ya bayyana cewa, da farko dai Seidu da abokan aika-aikarsa sun bukaci N5m daga wajen mahaifin yaron, amma daga baya sai suka sasanta a N300,000 saboda rokonsu da mahaifin yaron ya dinga yi.

Kamar yadda Oyeyemi ya sanar, lamarin ya faru ne a ranar 11 ga watan Disamba 2019, yayin da mahaifan yaron suka kai kokensu ofishin ‘yan sandan yankin da ke Ilupeju, Abeokuta, cewar anyi garkuwa da dansu. Oyeyemi ya ce, an kashe Abdulmalik ne saboda ya gane kawunsa.

Ya kara da kira ga jama’a da kada su amince da kowa saboda in har dan uwa zai iya wa dan uwa irin haka, ba shakka kowa zai iya yi. Amma babban wanda ake zargin ya bayyana cewa, shi bai bukaci kowa da ya sace dan yayansa ba. Kawai ya ga daya cikin masu garkuwa da mutanen ne tare da Abdulmalik. Amma bai yi wata yarjejeniyar garkuwa da shi ba.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN