Yadda iyaye suka daure hannayen yaro kuma suka watsa masa barkon a fuska

Mun sami rahotun cewa iyayen wani yaro sun daure hannuwansa a sama kuma suka watsa masa dakakken bakono a fuska a birnin Lagos.

Mujallar ISYAKU.COM ya samo cewa yaron mai suna  Daniel Ogunbona iyayensa na jini suka daure shi, kuma ba a fadi dalilin yin haka ko laifi da ya yi aka yi masa irin wannan danyen hukunci ba. Sai dai mun samo cewa lamarin ya faru ne a gida mai lamba 35 da ke kan titin Kokumo a unguwar Alimoso da ke birnin Lagos.

TSOKACI
Wanna danyen hukunci mataki ne da babu shakka zai iya zama sanadin kangarewar yaro zuwa mataki na rashi shakka balle tsoron hukunci kan laifi da zai iya aikatawa nan gaba.
Wajibi ne iyaye su kaurace wa irin wannan hukunci ganin cewa ya yi matukar tsauri duk da yake ba a fadi ainihin laifi da Daniel ya aikata ba.
Watsa dakakken barkono a fuskar yaro karami bayan an daure shi, wani babban hukunci ne da ko balagagge mai koshin lafiya ba safai zai iya jurewa ba balle karamin yaro.
 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post