Yadda Allah ya tona asirin wasu barayin mutane a wata jihar arewa

Allah ya tona asirin wasu masu satar mutane bayan wanda suka sace ya kira yansanda marmakin ya nemo N1m da ya yi alkawarin zai kawo.

Ahmadu Ibrahim wanda yake cikin mutum 5 da yansandan jihar Gombe suka gabatar wa manema labarai ya ce, wanda suka sace mai suna Gidado Jungudo, ya bukaci su sake shi domin ya je ya nemo N1m da suka bukata.

Bayan sun sake shi domin ya nemo kudin, sai Gidado ya garzaya wajen yansanda ya gaya wa DPO na yansandan Dukku, wanda ya sa yansanda suka bazama tare da masu farauta cikin daji inda suka gano maboyar barayin mutanen.

Yansanda sun yi nasarar kama  Audu Umar mai shekara 28, da Ibrahim Ahmadu mai shekara 25, daga kauyen Lapiya a Dukku, yayin da saura suka tsere.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post