Yadda aka yi cushen naira biliyan 264 cikin kasafin kudin 2020 da Buhari ya sa hannu

Rahotun Legit Hausa

A watan Oktoba, lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin dokar kasafin kudin shekarar 2020 a gaban majalisar hadin gwiwa na dattawa da wakilai, ya gabatar da naira tiriliyan 10.3 ne a cikin kudirinsa.

Amma kuma a lokacin da ya sanya hannu a kudirin don ya zama doka a watan Disamba, bayan nazarin majalisar okokin kasar, ya sanya hannu ne a kan kudirin da ya kunshi jimlar naira tiriliyan 10.6, wato an samu karin da ya kai na naira biliyan 264.

Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawar kasar, Ibrahim Barau, wanda wannan bayani ya fara fitowa daga bakinsa, ya ce anyi wannan cushe ne domin toshe gibin da aka samu wajen samar da ayyuka a kasar.

A bisa ga rahoton jaridar Premium Times, babban birnin tarayyar kasar Abuja ya fi samun kaso mai tsoka a cikin hukumomi da ma’aikatun kasar a kasafin kudin bana. Tun da farko shugaba Buhari ya kasafta wa Abuja naira biliyan 28.4, amma da kudirin kasafin kudin ya zama doka, sai jimillar kudaden ya karu zuwa naira biliyan 62.41.

Duk da cewa birnin Abuja na fuskantar kalubale sakamakon lalacewar da hanyoyi suka yi, za a yi amfani da naira biliyan 37 wajen gyarar majalisar dokokin kasar. A shekara mai kamawa, gyarar ginin majalisar dokokin kasar kawai zai lakume kudade fiye da wadda hanyoyin gwamnatin tarayya a fadin kasar za su lakume.

Idan aka lura da gaba daya kasafin kudin, za a gane cewa kusan dukkannin ma’aikatu da ke kasar sun samu kari daga majalisar dokoki, abin da wasu masharhanta ke kira cushe. Read more: https://hausa.legit.ng/1288047-yadda-aka-yi-cushen-naira-biliyan-264-cikin-kasafin-kudin-2020-da-buhari-ya-sa-hannu.html

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN