Legit Hausa
Jami'an hukumar 'yan sandan kasar Kenya ta cafke wata mata mai suna
Mercy Wanjiru wacce ake zargi da soka wa mijinta mai suna Kevin Kuria
wuka a kirji saboda ya hana ta barin gidansu na aure da sunan yaji.
Lamarin ya faru ne ranar Alhamis, 12 ga watan Disamba, a yankin Nakuru
dake kasar Kenya yayin da Mercy ta kwashe kayanta domin barin gidan
mijinta bayan fada-fadacen da suka saba yi sun ki ci sun ki cinye wa.
Ganau ba jiyau ba sunce Mercy wacce ta soki mijinta a kirji ta ce ta
yi hakan ne domin kokarin kare kanta bayan da mijinta, Kelvin, ya nemi
sukarta da wuka. Daniel Thiongo ya ce: "An ga akwatinta dankam da kaya
amma mijinta ya hana ta tafiya, a lokacin da aka kirani don insa baki
domin sulhunta su.
Amma da na isa gidan sai naga Kelvin a kwance a
kasa, jini yana zuba daga kirjinsa." An kara gano cewa, wacce ake
zargi da kisan kan ta dinga kiran makwabta da abokai don neman
taimakon a kaishi asibiti.
An mika gawar mamacin zuwa asibitin Nakuru
don adana ta, yayin da ita kuma Mercy aka garkame ta a ofishin 'yan
sanda. Kwamandan ofishin 'yan sandan Nakuru, Stephen Matu ya ce: "A
halin yanzu, ana cigaba da bincike kuma za a mika wacce ake zargi
gaban kuliya a ranar Juma'a domin ta fuskanci tuhume - tumen da ake yi
mata.