Mutum 28 yan gida daya sun mutu sakamakon wani hadarin mota a jihar Bauchi

Legit Hausa

Wasu mutane 28 yan gida daya sun mutu a sanadiyyar wani mummunan
hadarin mota daya rutsa dasu a jahar Bauchi yayin da suke kan hanyarsu
ta zuwa garin Yola na jahar Adamawa a ranar Alhamis, 12 ga watan
Disamba.

Jaridar Punch ta ruwaito hadarin da ya auku a kan babban hanyar Bauchi
zuwa Ningi ya yi muni matuka inda ya kona mutanen 28 kurmus, sai dai
gawayinsu kadai aka iya tattarowa.

Da majiyar ta gana da wani dan uwan mamatan, kuma sakataren kungiyar
yan jaridu reshen Arewa maso yamma, Abdullahi Yamadi ya tabbatar da
aukuwar lamarin, inda ya bayyanashi a matsayin lamari mai matukar
bakanta rai.

"Da gaske ne lamarin ya faru, kuma dukkaninsu yan uwana ne, suna kan
hanyarsu ta zuwa Yola a jahar Adamawa ne domin ziyarar yan uwa da
abokan arziki a lokacin da hatsarin ya auku, ka san bayan an yi girbi
mutane su kanyi amfani da wannan dama wajen tafiye tafiye.

"Sun fito ne daga Dutsanma ta jahar Katsina, suka shiga Jigawa, sun
shiga Bauchi kenan motarsu ta yi gaba da gaba da wata mota dake
tahowa, su 29 ne a cikin motar, dukkaninsu sun mutu, banda direba."
Inji shi.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto rundunar Yansandan
jahar Bauchi bat ace uffan game da lamarin ba.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta ma
gwamnatin kasar Nijar, tare da bayyana alhininsa bisa kisan da wasu
gungun yan ta'adda suka yi ma dakarun Sojojin kasar Nijar guda 63 a
garin Inates dake iyaka da kasar Mali.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa,
Malam Garba Shehu a ranar Laraba, 11 ga watan Disamba, inda yace yan
ta'addan sun fito ne daga kasar Mali, suka Nijar inda suka kashe
Sojoji 63, ba'a san inda 34 suka shiga ba.
Previous Post Next Post