Tsananin kishin wata mata: Matashi ya kashe magidanci bayan ya caka masa wuka

Wani magidanci mai suna Charles, ya mutu bayan abokin hamayyarsa mai shekara 35 mai suna Eyo Eketen ya caka masa wuka sau da dama.

Jim kadan bayan isar Charles gidan dadironsa ne da ke hanyar Nikton, a Kpansia domin shakatawa, sai Eyo ya je ya dinga caka masa wuka  a fusace kuma yana zagi yayin da yake ta caka wa Charles wuka.

An kama Eyo ne bayan dadiron Charles ta gan Eyo yana ta caka wa Charles wuka sai ta yi kururuwa har makwabta suka zo suka kama Eyo.

Tuni yansanda suka yi awon gaba da Eyo kuma yana amsa tambayoyi a wajen yansanda a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post