Gidan Talabijin na Igbere TV ya labarta cewa wata mata ta haura katangan wani gida ta ketare ta shiga ta saci buhun shinkafa a kudancin Najeriya, amma sai masu gida suka kamata dumu dumu da buhun shinkafa da ta sata.
Sai dai marmakin masu gida su yi mata duka ko su tozarta ta, sai suka tattaro kudi a tsakaninsu mai taro da sisi akta tara aka bata tare da buhun shinkafa da ta sace domin ta je ta ciyar da yaranta.
Allah sarki. Wannan yunwa ne ko talauci da zai sa babban mace kamar wannan ta ketare katangar wani gida domin ta saci buhun shinkafa?
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari