Sayar da tabar wiwi a jinin jikina yake, da wuya in daina sayarwa - Dilan tabar wiwi

Wani mutum mai suna Umaru Shehu ya ce shi fa sayar da tabar wiwi a jinin jikinsa yake, kuma fa da wuya ya fasa sayar da tabar. Umaru ya furta wadannan kalamai ne yayin da yake bayani wa jami'an hukumar NDLEA bayan sun kama shi da 1,072KG na tabar wiwi.

Dan shekara 55, Umaru ya fada hannun jami'an NDLEA ne a hanyar Mokwa da ke karamar hukumar Mokwa a jihar Niger. Jami'an hukumar sun yi nassarar cafke Umaru ne bisa wasu bayanan sirri.

Wanda aka kama ya fito daga Kurkuku ranar 8 ga watan Oktoba bayan ya shafe shekara daya a Kurkuku, sakamakon kama shi da Kotu ta yi da laifin sayar da wiwi, amma kuma ya sake aikata laifin kuma aka sake kama shi.

Umaru ya ce " Yana da matukar wuya in daina sayar da wiwi domin abin yana a cikin jinin jikina ne".

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post