Saurayi ya kashe mahaifinsa a cikin Masallaci da adda, Kotu ta ce a kashe shi | ISYAKU.COM

Wata babban Kotu a jihar Bauchi ta yanke ma wani matashi mai suna Umaru Jauro-Ori hukuncin kisa ta hanyar ratayawa har ya mutu, bayan ta same shi da laifin kashe mahaifinsa a cikin Masallaci a kauyen Mai aduwa da ke karamar hukumar Misau a jihar Bauchi.

Jastis Aliyu Usman ya yanke wa Umaru wannan hukunci ne bayan ya saurari shaidu da mai gabatar da kara ya gabatar wa Kotu, tare da sauraron shaidun wanda ake tuhuma.

Mai gabatar da kara Hussaini Magaji ya shaida wa Kotu a baya cewa, wanda ake tuhuma ya je cikin Masallaci a kauyen Mai'aduwa inda ya sami mahaifinsa yana Salla ,ya kuma sare shi a kai da kafada da adda.

Sakamakon haka mahaifinsa ya sami munanan raunuka kuma aka garzaya zuwa babban Asibitin Misau da shi inda ya mutu sakamakon raunuka da ya samu bayan kwana daya yana jinya a Asibitin.

Alkalin ya ce, shaidu sun gaya wa Kotu cewa marigayin ya raba gadonsa ga Umaru da sauran yan uwansa, amma sai Umaru ya bar gida ya shiga Duniya babu wanda ya san inda ya shiga har tsawon wata 10. Kwatsam sai ga shi ya bayyana a Masallaci kuma ya sare mahaifinsa lamari da ya zama ajalin dattijon.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post