Sarki Sanusi ya karbi nadin da Ganduje ya yi masa na shugaban Majalisar Sarakuna | ISYAKU.COM

Sarki Muhammadu Sanusi na 2 a yau Juma, ya karbi nadin da Gwamna Ganduje ya yi masa a matsayin shugaban Majalisar Sarakunan jihar Kano wanda ya kunshi Masarautu guda biyar.

Sanarwar wadda aka wallafa a shafin Twitter, na Peacock ya ce, Sarkin ya amsa wannan nadi ne ranar Juma'a 20 ga watan Disamba.

A baya dai, mun labarta maku cewa, Gwamna Ganduje ya ba Sarki Sanusi kwana biyu, domin ya yi nazari ko zai amsa wannan nadi da Ganduje ya yi masa.DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post