Kotu ta jefa jigon APC a Kurkuku kan yi wa Gwamnan PDP kazafi

Legit Hausa

Kotun Majistare da ke Bauchi ta bayar da umurnin tsare jigo a
jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Bauchi, Umar
Mohammed Mai Fata a gidan gyaran hali kan kazafi da ya yi wa gwamna
Bala Mohammed na kashe naira biliyan daya daga asusun gwamnati don
zaben jihar Bayelsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Dan sanda mai shigar da kara, Sufeta Ayuba Danladi da ya shigar da karar a madadin
kwamishinan 'yan sanda na jihar ya shaida wa kotu cewa Mai Fata a
cikin wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo ya yi ikirarin cewa
gwamna Mohammed ya dauki naira biliyan daya daga asusun gwamnatin
jihar Bauchi domin amfani da shi a zaben gwamnan jihar Bayelsa inda
aka nada shi shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamnan
PDP a jihar Bayelsa.

Sai dai bayan kimanin mintuna 30 da lauyan wanda
aka yi karar ya fita daga kotu kuma bai dawo ba, mai shigar da karar
ya bukaci kotu da dage cigaba da karar har zuwa lokacin da lauyan
wanda aka yi karar ya shirya a cigaba da shari'ar.A bangarenta,
alkaliyar kotun ta Majistaren, Safiya Doma ta dage cigaba da sauraron
shari'ar zuwa ranar 23 ga watan Disamban 2019 kuma ta bayar da umurnin
a bawa wanda ake zargin masauki a gidan gyaran hali har zuwa lokacin
da za a cigaba da zaman sauraron shari'ar.
Previous Post Next Post