• Labaran yau


  Kalli abin da yan maza suka yi ma wata mata a filin jirgi

  Wata mata ta gamu da tsangwama daga wasu mutane a filin jirgin saman Kotoka a kasar Ghana sakamakon wani mattsattsen wando da ta saka wanda ya bayyana surar halittan wadataccen bayanta. Bisa wannan dalili jama'a suka yi sha'awan abin da suka gani a jikin matar kuma suka dinga daukanta hoto da bidiyo ba tare da yardarta ba.

  Wata wanda matar ke tare da ita, ta yi ta kokarin kare bayan abokiyar tafiyarta, amma haka ya gagara ganin yadda maza suka dinga binta a baya, har da wasu da ke sanye da tufafin aiki, wanda yake kama da na ma'aikatan filin jirgin.

  A cikin bidiyon kuwa, an gan wani mutum da ko a jikinsa bai damu ba, wanda ke janye ta akwati mai taya, tare da matan guda biyu suna tafiya.

  KALLI BIDIYO A KASA:  TSOKACI

  Ya zama wajibi mata su dinga sa tufafi da ya dace da addini da kuma al'ada, wanda zai boye surarsu, domin wannan bidiyo daya ne daga cikin dubban ababe da ke faruwa da mata matukar suka yi irin wannan shiga kuma suka yi cudanya da maza. Allah ya kiyaye mu da zuri'armu.

  DAGA ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli abin da yan maza suka yi ma wata mata a filin jirgi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama