Jerin sunayen Gwamnoni 5 da suka fi shahara a shekarar 2019 | ISYAKU.COM

Legit Hausa

Akwai gwamnoni kuma akwai gwamnoni a Najeriya. Wasu gwamnonin ba a jin
duriyarsu, wasu kuma suna kan gaba a kafofin yada labarai saboda irin
aikinsu. A duk shekara, wasu gwamnonin kan yi zarra saboda wasu
dalilai.

A shekarar 2019, wasu gwamnonin sun zama zakarun gwajin dafi.
Uku daga cikin zakarun gwajin dafi a cikin gwamnonin, wannan shekarar
suka fara hawa karagar mulki yayin da sauran sun kasance a mulki tun
shekarun da suka gabata.

A wannan rubutu, Legit.ng ta tattaro muku
gwamnoni 5 na Najeriya da suka yi zarra a 2019. Sun hada da:

1. EmekaIhedioha Tsohon kakakin majalisar tarayya ne kuma ya hau mulkin jihar
Imo a ranar 29 ga watan Mayu. Alamu sun nuna cewa, tsohon dan
majalisar tarayyar yana gina jihohin Kudu maso Gabas, yankin da ya sha
wuyar rashin shugabanci nagari a shekaru takwas da suka gabata. Duk da
hankalinsa ya dauku a farkon hawarsa mulki sakamakon gudumuwar Owelle
Rochas Okorocha. Ya mayar da hankali kan shugabancin jihar daga baya.
Ya yi suna ne sakamakon fallasar da ya dinga na wadanda suka gabace
shi.

2. Seyi Makinde Dan siyasan mai shekaru 51 Injiniya ne. Makinde
ya bayyana cewa duk wani lamarin da ya danganci shugabanci nagari, toh
yana da hannu a ciki. Makinde ya fara bayyana kadarorinsa, lamarin da
kishiyoyinsa na siyasa suka kasa. Sabon gwamnan ya koma biyan albashi,
ya kashe tsagerun NURTW, ya fara fadada manyan titunan jihar kuma ya
zabi matashi mai shekaru 25 a matsayin kwamishina. Wannan ne kuwa ya
jawo wa gwamnan suna mai kyau.

3. Bello Matawalle Dan siyasar maishekaru 50 na daya daga cikin gwamnoni Arewa da ke haskawa. Gwamnan jam'iyyar PDP din ya fara yaki da 'yan ta'addan da suka gallabi jihar.
A yanzu gwamna Matawalle ya yi sasanci da tsagerun kuma sun ajiye
makamai tare da rungumar zaman lafiya. A cikin kwanakin nan ne gwamnan
ya datse biyan fansho ga wanda ya gada, lamarin da ya jawo jinjina
daga 'yan Najeriya gare shi. Babbar sa'a ce mutanen Zamfara, samun
jajirtaccen gwamnan.

4. Godwin Obaseki Gwamnan jihar Edo ya shiga
wannan sahun. Gwamnan ya dau lokaci yana gumurzu ne da wanda ya gada.
A maimakon fara shugabanci, ya mayar da hankali wajen yaki da siyasar
uban gida. Yakar Oshiomhole ba mummunan lamari bane, ballantana da ya
bayyana cewa yaki yake don mayar da hankali don shugabanci nagari.

5.Nasir El-Rufai Wannan gwamnan shi ake kira da dan baiwa. Masani ne a
harkar shuwagabanci kuma sanannnen dan siyasa ne. El-Rufai ya kasance
a kanun labarai saboda dalilin rawar da ya taka a siyasar 2019. Daya
tarihin da ya kafa a siyasa shine shiga daji da jami'ar tsaro don kama
'yan ta'addan da suka addabi yankin jihar. Ba a nan ta tsaya ba,
daukar mataimakiya mace ya kara wa gwamnan suna. Hatta tsohon shugaban
kasa Obasanjo ya jinjinawa tsarin shugabancin gwamnan. Ya kira shi da
'dan baiwa' kuma daya daga cikin mutane masu hazaka da ya yi aiki da
su.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN