IBB zai sake yin aure bayan kasancewa gwauro shekara 10

Rahotun Legit Hausa

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya shafe tsawon shekaru 40 yana zaune tare da matarsa, marigayiya Maryam Babangida, kafin mutuwarta a watan Disamba na shekarar 2009.

Marigayiya Maryam ta yi suna a Najeriya saboda irin tasirin da take da shi a kan mijinta da kuma soyayyar dake tsakaninsu. Kusan duk inda IBB yake yana tare da marigayiya Maryam, tamkar 'Zara' da 'Wata'.

A wata tattauna wa da jaridar 'The Sun' ta yi da IBB kuma ta wallafa a ranar Asabar, 28 ga watan Disamba, IBB ya bayyana cewa har yanzu bai daina jin radadin mutuwar Maryam ba duk da tsawon lokacin da ya shude tun bayan komawarta ga mahaliccinta.

Sai dai, duk da irin kewarta da jin radadin rayuwa babu Maryam a tare da shi, IBB ya bayyana cewa yana son zai sake yin aure. IBB ya kara da cewa da gaske yake yi yana son zai sake yin aure saboda tsufa yake kara yi, a saboda haka akwai lokacin da bukatar abokiyar zama ba zai yi masa wata rana ko amfani ba.

Da wakilin jaridar 'The Sun' ya tambaye shi a kan koda gaske yana son sake yi aure ko kuma dai fada kawai yake yi kawai da wasa, sai IBB ya ce, "har yanzu amsa ta a kan batun aure bata sauya ba, watau 'Eh' ina da niyyar sake aure, kawai ina tunani ne har yanzu a kan lamarin."

Da aka tambaye shi ko akwai wata da yake burin aure a halin yanzu, sai IBB ya amsa da cewa, "a'a, ni babu wata mace a raina da nake buri ko fatan aure, amma tabbas ina da niyyar sake yin aure saboda kullum tsufa nake kara yi, idan ban yi aure kwana kusa ba, zan wuce lokacin da zai yi min amfani.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN