Hukumar Hisba a jihar Zamfara ta kama wani jami'in dansanda tare da yan mata uku a cikin dakin wani Otel. Shugaban hukumar Dr. Atiku Zawuyya ya ambato haka yayin da ya gabatar da wadanda aka kama a harabar hukumar a Gusau ranar Litinin.
Kampanin dillancin labarai na Najeria NAN, ta ruwaito cewa Dr Zawuyya ya ce an kama wasu mutane tare da dansanda da ke aiki a ofishin yansanda na Central Police Station, domin sun saba dokokin shari'a na jihar Zamfara.
Hakazalika Zawuyya ya ce daya daga cikin yan mata da aka kama ta fito ne daga jihar Kaduna, yayin da ragowar biyu daga cikin matan yan gida daya ne a jihar Zamfara.
Ya kara da cewa, an sha gargadin mai Otel da aka kama mutanen, cewa ya daina samar wa irin wadannan mutane matsuguni a cikin wannan Otel tare da yin biyayya ga dokokin gudanar da Otel na jihar, amma ya yi kunnen uwan shegu da gargadin.
Bayan Hisba ta kama Manajan Otel da aka kama mutanen, Zawuyya ya ce hukumar za ta gurfanar da su a gaban Kotu da zarar ta kamala bincike.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari