Hassada ya sa matasa sun banka wa shago,gida da motocin dan kasuwa wuta | ISYAKU.COM


A ko da yaushe dan adam yana gamuwa da ababe da ke faruwa ba zato ba tsammani, wani sa'ilin kuwa, lamarin ma na rainin hankali ne tare da ban haushi. Da tsakar ranar yau, mun sami labarin cewa wasu matasa masu tsananin hassada sun banka wa shagon wani bawan Allah wuta, inda dukiya na miliyoyin naira suka kone kurmus, saboda yana samun kasuwa kwarai fiye da sauran yan kasuwa a garin Agubia Ikwo cikin jihar Ebonyi..

Wanda aka kaiwa harin Mr Nwali Igberi Chinedu (Uwabuakpi) mai shekara 26, ya gamu da tashin hankali bayan matasan sun kai mashi hari suka raunata shi da adda, bayan sun sare shi a kai, ba gaira ba dalili, suka kone masa babur da motocinsa, daga bisani suka banka wa shago da gidansa wuta har wuta ya kone gidan kurmus.


Yanzu haka Mr Nwali na kwance yana jinya a Asibiti, yayin da aka bar iyalinsa da kangon gida da shago domin komi ya kone.


Rahotanni sun ce yansanda sun damke wasu daga cikin matasa da ake zargin sun aikata wannan aiki.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN