Duba abin da ya faru bayan Tinibu da Atiku sun hadu a filin jirgi

Dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 karkashin jam'iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar sun yi gamuwar bazata tare da jagoran jam'iyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu, a kebantaccen dakin manyan baki a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke birnin Abuja ranar Asabar 15 ga watan Disamba.

ISYAKU.COM ya samo cewa Tinibu na kan hanyarsa ce ta zuwa Jami'ar Ibrahim Babangida da ke Lapai a cikin jihar Niger domin karbar Digirin girmamawa, yayin da Atiku ke kan hanyarsa ta zuwa wajen daurin aure tare da rakiyar Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri.


SHARHI

Abin kulawa ga yan Najeriya musamman kasar arewa dangane da wanna lamari shine yadda mutanen guda biyu suka karbi junansu cikin mutunci, martaba da girmamawa, ba tare da nuna wani alamar damuwa ko gaba na siyasa ba. Duk da yake Atiku ya sha kashi a zaben 2019 karkashin jam'iyar PDP bayan Buhari ya ci zaben karkashin jam'iyar APC.

Ya rage ga talaka ya san inda kansa ke ciwo yanzu a harkar siyasar arewacin Najeriya, da Najeriyar kanta a siyasance. Ba gaba, ba tsangwama balle rigima tsakanin manyan yan siyasa, sakamakon haka shi ma talaka kamata ya yi ya watsar da damuwa ta siyas.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post