Dole ne a kara farashin wutan lantarki a Najeriya - Inji Minista

 Legit Hausa

Bisa dukkan alamu nan da wasu kwanaki kadan ‘Yan Najeriya za su fara biyan farashin da ya zarce abin da su ka saba biya domin samun hasken wutar lantarki a kasa.

Gwamnatin tarayya ta na shirin kara farashin wuta a Najeriya da zarar ta kammala ayyukan da ake yi a fadin kasar inji Ministan harkar lantarki watau Injiniya Sale Mamman. Ministan ya bayyana cewa za a dada farashin shan wutan ne bayan an samu kari a kan yadda ake samar da wutar lantarki har ya zo ga kamfanonin da ke da alhakin rabo.

Sale Mamman ya nuna cewa farashin da ake shan wuta a kasar ya jawo cibaya a game da samar da lantarki zuwa ga masu bukata. Wannan ya sa dole za a kara farashin wutan. Mai girma Ministan ya yi alkawari cewa za a cigaba a sha’anin wutar lantarki da zarar gwamnatin tarayya ta kammala ayyukan wutan da ta ke yi a tasoshin da ke Najeriya.

 “Ayyukan da ake yi za su kara karfin wuta a Najeriya. Idan wuta ta gyaru, dole a kara farashi a fadin kasar, saboda dole a maida kudin da ake kashewa wajen samar da wutan” Injiniya Mamman ya shawarci ‘Yan Najeriya da su rika biyan kudin wutansu, tare da fadawa jama’a cewa gwamnati ta na daukar matakai na ganin lantarki ya inganta.

The Nation ta rahoto Ministan ya na wannan jawabi a Ranar 21 ga Watan Disamban 2019. Har yanzu dai wuta ya na cikin abin da ke ci wa ‘Yan Najeriya tuwo a kwarya.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN