• Labaran yau


  Cika shekara 40 a Birnin kebbi, kazafin Luwadi shi ne tukuici da na samu | ISYAKU.COM

  Ranar 23 ga watan Disamba ni Isyaku Garba Zuru na cika shekara 40 a ckin garin Birnin kebbi, sakamakon isowar mu a garin Birnin kebbi a 1980 bayan Mahaifi na ya zo garin Birnin kebbi sakamakon canjin wurin aikin soji da aka yi masa daga Kaduna.

  Sakamakon haka ya kasance sai dai in shiga in fita daga Birnin kebbi amma nan ne gida a wajena, duk da yake ni asalin Dan Zuru ne.

  A lokacin da nike karatu a makarantar Sakandare na Haliru Abdu a shekarun 1980, nan ne na fara fuskantar kalubale daga wasu dalibai yan asalin garin Birnin kebbi. Domin na sami wata dama da hukumar leken asairi na soji suka yi amfani da ni tare da wasu zababbun dalibai, da wata hukumar tsaro domin farautar yan LUWADI a garin Birnin kebbi, sakamakon yadda wani dan Luwadi ya keta mutuncin dan gidan wani soji, sakamakon fyade da ya yi ma yaron.

  Karanta yadda muka gudanar da aikin a nan: LATSA NAN

  Tun daga wannan lokaci aka sami wasu munafukai wadanda ayyukanmu ya zama tonon asiri ko fallasa ga ubanninsu, yan uwansu ko zuriyarsu, suka sa ni gaba suka dinga yadawa cewa Isyaku dan Luwadi ne bisa jahilci da rashin fahimtar inda aka dosa. Domin ina daya daga cikin dalibai da makarantar ke alfahari da su a wancan lokaci. Domin kasancewa na cikin dalibai da suka wakilci makarantar wajen DEBATE, QUIZ, da NEWS READING. har da kasancewa a Boy Scout.

  Babban abin haushi a nan shine yadda har yau wasu da basu san hawa balle sauka ba a garin Birnin kebbi suka dinga alakanta ni da kasancewa dan Luwadi bisa kazafi, sharri da kabilanci. Domin har yau babu waanda ke da kwakkwarar hujja cewa ni dan Luwadi ne, ko kuma an taba kamawa ko zartar da hukunci da ya danganci Luwadi a kaina.

  Hakazalika, idan har Isyaku dan Luwadi ne, lallai dan Birnin kebbi ne ya koya masa wannan aiki, to mi ya sa ba a ambaton yan Birnin kebbi da ake zargin cewa su ne suka koya wa Isyaku Luwadi? wannan tabbaci ne na kabilanci. Ina kira ga Dakarkari na kasar Zuru a ko ina suke a cikin Duniya su sani, ni Isyaku dan uwansu ba dan Luwadi bane kamar yadda Yahudawan Birnin kebbi suka yi mani kazafi.

  Kuma idan Isyaku dan Luwadi ne mi ya sa masu kira na dan Luwadi a garin Birnin kebbi basu tona mani asiri ba tun shekara 35 da suka gabata sai dai su dinga munafunci da bata suna wanda ya samo asali daga Fasikai zuri'ar yan Luwadi a garin Birnin kebbi..

  Gaskiyar lamarin shi ne, masani ne ni a kan harkar Luwadi a garin Birnin kebbi , kuma ina gargadin munafukai bata gari cewa babu zuri'a da bata haifi dan Luwadi ba a cikin masu kirana dan Luwadi a cikin garin Birnin kebbi. Irin wadannan mutane ne suka kirkiro kuma suka raya wajen fasikanci a Birnin kebbi suka sa ma wuraren suna JAHANNAMA ROAD, WAMAKO ROAD,ALU ROAD da sauransu, wanda duk waje ne da ake zargin ana aikata FASADI ko magama da ake haduwa da abokan aikata FASADI.

  Sakamakon haka a yau 23 ga watan Disamba 2019, ni Isyaku zan dinga kiran Fasikai da suke kirana dan Luwadi a garin Birnin kebbi da suna YAHUDAWAN BIRNIN KEBBI.

  A sani na, wadannan YAHUDAWAN Birni kebbi sun sha alwashin ci gaba da yi mani kazafi da bata mani suna ne domin in ji haushi in bar garin Birnin kebbi, wanda haka bai samu ba. Hakazalika irin wadannan mutane sun hada baki da masu tunani irin nasu suka karbe mani shaguna guda uku da nike kasuwanci a cikinsu a titin Ahmadu Bello a garin Birn kebbi, domin wai sai sun ga bayana a cikin Birnin kebbi.

  Har ila yau, irin wadannan mutane sun jagoranci shiryayyen munafunci suka nemi su kawo gaba tsakanina da yara da na koya masu aiki har na yi masu aure, amma Allah ya basu kunya. Hakazalika wadannan mutane sun haddasa yara kanana suka dinga ci mani mutunci a wajen sana'a ta, ciki har da yan gidan wata Kwatakwalli. Duk wadannan ababe na jure na bar wa Allah, domin mai hakuri mawadaci ne inji malam Bahaushe.

  Fiye da shekara 35 kenan amma ake ta bata mani suna a garin Birnin kebbi kadai, alhalin na zauna wasu garuruwa da jihohi, kuma babu inda aka taba alakanta ni da wannan lamari sai a agarin Birnin kebbi.

  Makwabta na sun shaida cewa ban taba alakanta kaina da irin wannan kazafi da aka yi mani ba a garin Birnin kebbi. Na kalubalanci jama'ar garin Birnin kebbi gaba daya domin nan ne kadai a duk garuruwan Duniya inda aka ci mani zarafi da wulakanci, cewa duk wanda yake da wata shaida cewa ni Isyaku dan Luwadi ne, don Allah ya zo ya yi bayani, har kyauta zan bashi. Idan kuwa babu, ni na barku da karfin zatin Allah ya saka mani.

  Isyaku Garba Zuru

  Domin kalubale, ra'ayi, ko shawa latsa nan ka tuntube mu isyakulabari@gmail.com  Facebook @isyakulabari

  DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Cika shekara 40 a Birnin kebbi, kazafin Luwadi shi ne tukuici da na samu | ISYAKU.COM Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama