Buhari ya yi ganawar sirri da gwamna Bagudu, Badaru da Fayemi. Duba dalili | ISYAKU.COM

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja sun ce shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri tare da wasu Gwamnonin jam'iyar APC guda uku a fadar gwamnati .

Jaridar Legit Hausa ta ruwaito cewa Buhari ya fara gana wa ne, a bayan fage, tare Fayemi, gwamnan jihar Ekiti. Daga bisani Buhari ya gana da gwamna Bagudu wanda ya samu rakiyar takwaransa, gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar.

Legit.ng ta ruwaito cewa, fadar shugaban kasa ta ce babu wani aibu idan akwai 'miyagu' zagaye da Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Fadar ta bayyana cewa, akwai irin mutanen a kowacce gwamnati a fadin duniya.

Fadar ta kara da jaddada cewa, akwai bukatar a kafa dokar soshiyal midiya, ganin cewa rashinta na kawo cin zarafi ga mutane. Babban mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa a kan yada labarai, Malam Garba Shehu, ya tabbatar da hakan ne yayin ganawa da manema labarai a Abuja. Ya ce,

"Babu gwamnatin da aka taba samu a kasar nan da babu wasu mutane da ake zargi da zama miyagu a gwamnatin. Kuma hakan ya zama dole ne saboda kowacce gwamnati ko shugaban kasa yana da mataimaka."

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN