Birnin kebbi: An gudanar da kasaitaccen tattakin Maulidi

Dubu dubatan jama'a mabiya Dariku, sun gudanar da wani kasaitaccen tattakin Maulidin Manzon Allah (SAW) a garin Birnin kebbi babban birnin jihar Kebbi da safiyar Asabar 7 ga watan Disamba 2019.

Lamari da ya mayar da garin Birnin kebbi tamkar bikin Sallah, sakamkon yadda yara, mata, matasa yan Darika da wadanda ba yan Darika ba suka fito zuwa bakin manyan hanyoyin titi domin su kalli wannan tattaki.

Masu tattakin sun yi ta rera wakokin yabon Manzon Allah, yayin da wasu ke amfani da sautin kida daga na'urorin sauti. Kowane Zawiyya sun yi amfani da kalar tufafi daban daban, wanda haka ya kara wa tattakin armashi tare da birgewa.

An fara tattakin ne da misalin karfe 10 na safe daga gidan Khalifa , suka biyo ta tsohon garin Birnin kebbi, suka bullo ta Kofar Kola, daga bisani suka mike ta hanyar Illela Yari. Daga nan ne suka mike kan titin Makerar Gandu, sai suka biyo ta titin Rafin Atiku, suka kuma juya a Shataletalen Masallacin Haliru Abdu suka mike zuwa Shataletalen Haliru Abdu  har zuwa karshen tattakin da ya kare a gidan Khalifa inda suka fara.

An gudanar da tattakin lafiya a yanayi da ya ja hankalin dubban mutane a cikin garin Birnin kebbi da ya kasance tamkar bikin Babban Sallah sakamakon wannan tattaki.

KALLI BIDIYO;

 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post