• Labaran yau

  Ba mu daukan yan boko haram da suka tuba aikin soji - Rundunar sojin Najeria

  Rundunar sojin Najeriya ta musanta jita-jitan cewa rundunar tana daukan tsofaffin mayakan boko haram da suka tuba aikin sojin Najeriya

  A wata sanarwa da ta fito daga Daraktan watsa labarai na rundunar Brigadier Onyema Nwachukwu, ya musanta wannan zargi da jita-jita, wanda ya alakanta da fitowarsa daga rashin bincike ingantacce daga mutane da basu san gaskiyan abin da ke faruwa ba.

  Ya kara da cewa fiye da mayakan boko haram 250 da suka tuba suka mika kansu ga rundunar soji ne , aka ba horo na musamman tare da hadin guiwa da Malaman addinai, Sarakunan gargajiya, kuma daga bisani suka sake shiga al'umma domin gidanar da rayuwa kamar kowa.

  DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari

  Twitter.com/isyakulabari
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ba mu daukan yan boko haram da suka tuba aikin soji - Rundunar sojin Najeria Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama