Ba da mu ba a wakar batanci ga shugabanni: Matasan mawakan jihar Kebbi

Kwana daya bayan wasu mawaka a jihar Kebbi sun saki wata wakar kalubale ga wani babban dan siyasa a jihar, wasu matasa da suka kira kansu da Matasan Mawakan jihar Kebbi sun yi raddi ta hanyar rera wata waka da suka kalubalanci mawakan farko.

Mujallar ISYAKU.COM ya gano cewa dama akwai azazza a tsakanin kungiyar mawaka na jihar Kebbi, wanda ya rabu gida biyu. Daya bangaren shine bangaren manyan mawaka, sai kuma bangaren Matasan Mawaka.

Kokari da muka yi na jin ta bakin Manyan mawaka na jihar Kebbi domin su tofa albarkacin bakinsu a wannan matsala ya ci tura kawo yanzu. Amma Matasan Mawaka na jihar Kebbi, sun yi kakkausar raddi a waka da kuma faifen bidiyo.

KALLI BAYANIN RADDI:DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post