An rantsar da sabbin Alkalan Majistare guda 9 a jihar Kebbi, duba sunayensu

Mukaddashin babban Jojin jihar Kebbi Jastis Sulaiman Ambursa, ya rantsar da sabbin Alkalan Kotunan Majistare guda tara a Birninkebbi ranar Laraba.

Jastice Ambursa ya bukaci sabbin Alkalan Majistaren su kasance masu aiki tukuru tare da bin ka'idara aikin shari'a.

" Kuyi kokari ku yi adalci domin kuna da matakan doka bisa tsarin shari'a da za ku bi domin gudanar da aikinku" a cewar Jastice Ambursa.

Ya kuma kara da cewa " Ku gudanar da aikinku tukuru bisa tsarin doka, kuma ba a sa ku yi wani abu da baya cikin tsarin doka ba ga kowa, face gudanar da wanzuwar tsarin doka wanda shi ne ginshikin gwamnatin adalci"

A nashi jawabin godiya a madadin sabbin Alkalan Majistaren, Abubakar Muhammad, ya mika godiyarsu ga kungiyar Majistare na Najeriya reshen jihar Kebbi, tare da ma'aikatar shari'a na jihar Kebbi

Alkalan Majistare da aka rantsar sun hada da: Abubakar Ahmed, Sanusi Abubakar, Sanusi Diri, Attahiru Zagga, Fatima Yeldu, Aishatu Dabai, Usman Dayyabu, Abubakar Rugga and Adamu Libata
 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post