An mayar da wutan lantarki a Birnin kebbi da jihar Kebbi bayan janye yajin aikin NUEE

An mayar da wutan lantarki a garin Birnin kebbi da kewaye sakamakon janye yajin aiki da kungiyar NUEE ta kasa ta yi, domin jawo hankalin gwamnatin tarayya a kan kangin da ma'aikatan wutan lantarki ke ciki.

Yanzu haka TCN na kan raba wutan lantaki a garin Birnin kebbi da kewaye kamar yadda aka saba.

Idan baku manta ba, Mujallar ISYAKU.COM  ya ruwaito maku labarin cewa an sami daukewar wutan lantarki a garin Birnin kebbi da jihar Kebbi gaba daya sakamakon yajin aiki da kungiyar NUEE ta shiga daga karfe 12 na safiyar Laraba zuwa Alhamis.
 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post