An kama mutum 24 da suka yi smogal shinkafa daga kasar waje | ISYAKU.COM

Jami'an sojin ruwa na Forward Operation Base (FOB) da ke Ibaka a karamar hukumar Mbo na jihar Akwa Ibom, sun kama mutum 24 da ake zargi da satar shigowa Najeriya da buhu 1.831 na shinkafa daga kasar Cameroun.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shugaban rundunar FOB, Navy Captain Peter Yilme, ya ambato haka ranar Lahadi, ya ce jami'ansa sun kama jiragen ruwa na katako guda 5, dankare da haramtaccen buhuhunan shinkafa 50kg daga kasar Cameroun.

Ya kuma kara da cewa an gudanar da kamen ne a wurare hudu wanda sojin ruwa suka gudanar yayin da suke sintirin bincike a jiragensu na ruwa da aka girka wa manyan bindigogi.

Hakazalika ya kara da cewa ranar 27 ga watan Nuwamba, jami'an sojin ruwa sun kama mutum hudu da buhun shinkafa 50kg guda 294 a cikin jirgin ruwa. Ranar 5 ga watan Disamba kuma, jami'an sun  kama mutum takwas da buhu 87 na shinkafa, sai kuma ranar takwas da goma sha daya ga watan Disamba, an kama mutum bakwai dauke da buhu 1.270 na shinkafa a cikin jirgin ruwa, da kuma wasu mutum takwas a jirgin ruwa dauke da buhu 172 na haramtaccen shinkafa daga kasar ta Cameroun.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/DTV1WsH2ypv0WtRujXbA0F SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN