An kama dan shekara 52 yana lalata da gawar wata budurwa a Mutuware | ISYAKU.COM

An kama wani mai bincike kan gawaki turmi tabarya yana lalata da gawar wata budurwa a dakin ajiye gawa.Rahotanni sun ce wanda aka kama mai suna  Wanderley dos Santos Silva  mai shekara 52 ya yi haka ne domin nuna jin dadinsa bayan kungiyar kwallon kafa da yake goyon baya ta ci wasan kwallon kafa da ta buga. Wanna lamarin ya faru ne a kasar Brazil.

Wani dansanda da ke sashen kula da bayanan bincike kan gawaki ne ya kama Santos turmi tabarya yana lalata da gawar budurwar yayin da ya shiga dakin ajiye gawa domin ya sami bayani kan wata gawa. Dansandan ya kama Santos ne yayin da wani abokin Santos yana tsaye kuma yana ganin abin da Santos ke aikatawa a cikin dakin.

Yanzu haka hukumar Asibitin tare da yansanda suna gudanar da bincike kan wannan danyen aiki. Shugaban Asibitin ya dakatar da Santos daga aiki yayin da ake ci gaba da bincike.
 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post