Zargin sayar da Tramal: Sojin kasar Cameroon ya bindige dan Najeriya har lahira

Wani dan kasuwa dan asalin Najeriya ya gamu da ajalinsa a kasar Cameroon inda yake kasuwancin sayar da magani (Chemist) . Wani sojin kasar Cameroon ya kama Uchenna Mouka daga cikin shagonsa na Chemist a bayan kasuwar Ntarikon da ke Bamenda, tare da sauran jami'an soji, daga bisani wani soji ya bindige shi har lahira a unguwar Foncha.

Sojin suna zargin Uchenna da sayar da kwayar Tramal wanda Asobitoci ke amfani da shi wajenn maganin ciwon jiki, amma kuma ake samun akasin haka sakamakon yadda wasu ke amfani da shi fiye da kima wanda ke sa t6sananin maye.

Ranar Asabar da ta gabata ne aka kai gawarsa kasar Najeriya daga kasar Cameroon, domin yan uwansa su binne shi. Ya mutu ya bar yara 4 da matarsa mai dauke da juna biyu.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post