Zanga-zanga ta barke a Kano kan sauke sabbin sarakunan Ganduje

Legit Hausa
Wasu mazauna jihar Kano sun tada zanga-zanga a kan sauke sabbin sarakunan jihar Kano da kotu ta yi a yau. Masu zanga-zangar sun nuna rashin jin dadinsu a kan wannan cigaban. Sun ce wannan yunkuri ne na dakile karuwar da suke yi daga sabbin masarautun da suke ta mora.
A yau Alhamis ne wata babban kotu da ke zama a jihar Kano ta soke kirkirarrun sarakuna 4 da masarautunsu na jihar Kano.
Alkalin kotun, Jastis Usman Na'Abba, ya yanke hukuncin cewa kirkirar masarautun tare da nada sarakunan masu darajar farko an yi ne ba bisa ka'ida ba.
Hakan na nufin yanzu sarki daya ne a jihar Kano.
Sabbin Sarakunan da aka tube wa rawuna sun hada Aminu Ado Bayero, wanda shine Sarkin Bichi. Ibrahim Abubakar a matsayin Sarkin Karaye, Tafida Abubakar II a matsayin Sarkin Rano da kuma Ibrahim Abdulkadir a matsayin Sarkin Gaya.
A halin yanzu dai gwamnatin jihar Kano na da kwanaki 90 don daukaka kara. Yin shirunta kuwa na nufin ta gamsu da hukuncin kotun.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post