Yanzu-yanzu: Kwastam ta haramta sayar da fetur ga gidajen mai dake da kusancin 20km da iyakokin Najeriya

Legit Hausa
Gwamnatin tarayya ta bakin hukumar hana fasa kwabri wato Kwastam, ta bada umurnin daina sayarwa gidajen mai dake kimanin kilomita 20 da iyakokin Najeriya man fetur.
Kwantrola Janar da hukumar kwastam, Hameed Ali, ya bada umurnin ne a jawabin da wani mataimakinda Chidi, A ya fitar ranar 6 ga Nuwamba, 2019 kamar yadda Legit.ng ta gani.
Jawabin yace: " Kwantrola Janar na kwastam ya bada umurnin cewa daga yanzu kada a sake sayarwa gidajen mai da ke da kusancin kilomita 20 da iyakokinmu komin kankancinshi."
"Saboda haka a na kira ga ku dabbaka umurnin kai tsaye."
A wani labarin, Kwantrola Janar na hukumar hana fasa kwabrin, Kanar Hamid Ali, ya ce rufe iyakokin Najeriya da akayi zai yi matukar taimakawa cigaban kasar.
Yace: "Wannan gwamnati ce wacce ta lashi takobin cewa wajibi ne mu gina Najeriya, mu ci kayan noman Najeriya."
"Kasar Sin da muke zuwa siyo kusan dukkan kayayyakin da muke amfani da su, shin kun san shekaru nawa suka rufe iyakokinsu? Sun rufe iyakokinsu na tsawon shekaru 40 kuma gashi yau sun girma. Shin baku son Najeriya ta girma ne?"
Hakazalika Shugaba Hukumar DSS, Magaji Bichi, ya ce rufe iyakokin da Najeriya da gwamnatin tarayya tayi ya taimaka wajen rage fataucin makamai kuma ya taimakawa jami'an tsaro wajen lura da shiga da ficen mutanen da ka iya zama kalubale ga zaman lafiyar kasa.
Mista Bichi ya bayyana hakan ne a taron yaye daliban ilimin leken asiri da Abuja.
Ya roki gwamnati ta sanyawa iyakokin katangar karfe har sai lokacin da abubuwa suka daidaita.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN