Yadda yan bindiga suka kashe wani dan kasuwa a garin Kaita na jihar Katsina - Rahotun musamman


Wasu yan b indiga da ake zaton masu sace mutane ne, sun kashe wani dan kasuwa Sa'adu Dan Bagalo yan awowi bayan sun sace shi a gidansa da ke garin Kaita a jihar Katsina.

Mujallar ISYAKU.COM ya samo cewa yan bindigan sun kai hari ne a gidan marigayin da karfe 1:42 na dare, kuma suka dinga yin harbin mai uwa da wabi a cikin iska, daga bisani yansanda suka fuskance su kuma aka yi ta artabu na barin wuta da bindigogi tsakanin yansanda da yan bindigan har tsawon awa biyu.

Haka zalika Mujallar ISYAKU.COM ya samo cewa sakamakon karfin wuta daga bindigogin yansanda, yan bindigan sun tsere tare da Sa'adu Dan Bagalo suka bi hanyar kauyen Bakiyawa, amma sai Sa'adu Bagalo ya yi kokarin tserewa sai yan bindigan suka harbe shi a baya, lamari da ya sa ya mutu n an take.

Sai dai Kakakin hukumar yansandan jihar Katsina SP Gambo Isah ya ce

 " Ranar 17 ga watan Nuwamba da misalin karfe 3 da minti 10 na dare, yan bindiga masu yawa dauke da bindigogi kirar AK47 sun dinga harbin mai kan uwa da wabi sun kai hari a gidan Alhaji Sa'adu Dan Bagalo mai shekara 50 a Kofar Kudu da ke karamar hukumar Kaita a jihar Katsina, kuma suka sace shi. Amma yansanda masu sintiri na Patrol na rundunar yansanda na Kaita, sun mai da martani ta hanyar kai dauki a gidan Alhaji Sa'adu Dan Bagalo, sai yan bindigan suka tsere, amma yansandan suka bisu har cikin daji. Bayan yan bindiga sun ga cewa ba zasu iya jure wa martanin yansanda ba, , sai suka kashe Sa'adu da wani mutum mai shekara 58 mai suna Bawale Inusa, kuma suka tsere zuwa cikin daji".

SP Isah ya tabbatar da cewa dansanda daya tare da wasu mutane biyu sun sami raunuka daban daban sakamakon artabu da yan bindigan.

" Yanzu haka masu bincike na yansanda suna tace dajin wannan yanki karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan yansanda sashen bincike DC CID KTS, domin ganin cewa an gano wadanda suka aikata wannan aika aikan".

An binne Alhaji Sa'adu Dan Bagalo tare da Bawale Inusa bisa tsarin addinin Musulunci.

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post