Yadda kuskuren hada kalaman turanci ya basar da matar wani Gwamnan arewa wajen taro

Wani faifen bidiyo da ke yawatawa a shafukan yanar gizo, ya nuna yadda uwargidan Gwamnan jihar Nassarawa Hajiya Silifa ta gamu da tuntuben harshe wajen karanta wani rubutaccen jawabi a wajen wani taro sau da dama, kafin daga bisani ta ketare wasu jawaban kuma ta mika wasu takardun ga wani mai yi mata hidima mata.

Tuni dai wannan lamari ya dauki hankalin ma'abuta amfani da intanet, musamman a zauruka da shafukan sada zumunta.A wannan faifen bidiyo, an ga Hajiya Silifa tana kokarin hada tare da furta wasu kalaman Turanci cikin yar sarkakiya.

Uwargidan Gwamnan tana kokarin yin jawabi ne a wajen taron kaddamar da shirin MMC a jihar Nassarawa.
 
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post