Yadda Buhari ya kauce wa yin musabaha da uwargidan Tinubu a wajen taro

Isyaku Garba Zuru

Wani faifen bidiyo daga babban birnin tarayya Abuja, ya nuna yadda shugaba Buhari ya kaurace wa yin musabaha da uwargidan Ahmad Tinibu wanda babban jigo ne a jam'iyar APC, lokacin da ya iso wajen wani taro a birnin Abuja.

Mujallar ISYAKU.COM ya lura cewa Ministan sadarwa Ali Pantami, ya kasance shinge a daidai lokacin da shugaba Buhari ke gaisawa da manyan jami'an gwamnatii da suka tarbe shi lokacin da ya isa wajen taron, cikin sauran manyan mutane da ke jere a wajen har da uwargidan Ahmad Tinubu.


Ali Pantami, wanda fitaccen mai fadakarwa tare da wa'azin addinin Musulunci ne, baya musabaha ta gaisawa da mace. Wanda haka ya haifar da zato mai karfi cewa ba mamaki kasancewarsa shinge a daidai gaban uwargidan Tinibu zai iya kasancewa dalili da ya sa shuaga Buhari bai yi musabaha da ita ba. 

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA Facebook.com/isyakulabari Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post