Wannan karo Buhari ya bar Najeriya zuwa Ingila ba tare da mika wa Osinbajo mulki ba


Legit Hausa

Yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tare a kasar Ingila inda ya ke sararawa har zuwa Ranar 17 ga Watan Nuwamba, ya bar Najeriya ba tare da ya mikawa mataimakinsa mulki ba.

Daga Birtaniya dai shugaban kasar ya sa a hannu a kan wani kudiri da majalisa su ka amince da shi. Ganin haka ya sa aka dawo da korafin cewa Abba Kyari ya na da ikon da ya zarce kima. Wannan mataki da shugaban kasar ya dauka ya dade ya na jawo surutu da ce-ce-ku-ce.

Yanzu dai Daily Trust ta kawo jerin wasu ayyukan da Yemi Osinbajo ya yi a lokacin da ya samu dama.

1.       EFCC: Ibrahim Magu Bayan wata tafiyar shugaban kasar ne Mataimakinsa ya aika takarda ga majalisa domin ta tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC. A karshe Sanatoci ba su yi hakan ba. 

2. CJN: Walter Samuel Onnoghen 

A farkon 2017 ne Farfesa Yemi Osinbajo ya aika sunan Walter Samuel Onnoghen gaban majalisa domin a tabbatar da shi a matsayin Alkalin Alkalai. Bayan tabbatar da shi, daga baya ya bar kujerarsa.

3. Tsige Lawal Daura daga DSS 

Wani babban matakin da Yemi Osinbajo ya dauka a lokacin da ya ke rike da Najeriya shi ne sauke Mista Lawal Daura daga kujerar shugaban hukumar DSS bayan jami’ansa sun zagaye majalisar tarayya.

4. SARS zuwa FSARS 

Haka zalika yayin da ya ke kan kujerar mukaddashin shugaban kasa, Osinbajo ya rusa hukumar SARS inda ya maida ta FSARS bayan koke-koken dinbin jama’a game da zaluncin jami’an tsaron a Najeriya. Ana rade-radin cewa wasu matakan da Osinbajo ya dauka sun hada shi fada da na-kusa da Mai gidansa. Dama can ana zargin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasan da rike madafan iko.
 

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN