Yadda aka cafke wasu yansandan SARS na bogi guda 2

Rundunar yansandan jihar Lagos ta cafke wasu yansandan sashen SARS na boge guda biyu wanda ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar Bakare Daudu domin su yi kame.

Wadanda aka kama sun hada da Ikechukwu Victor da Emeka Ewuzien. DPO na rundunar yansandan Ifako CSP Lasisi Iyunde ne tare da yansandansa suka kama mutanen guda biyu.

Kakakin hukumar yansandan jihar Lagos Elkana Bala, ya tabbatar da cafke mutanen guda biyu, ya kara da cewa an sami takardar shaidar ID card na yansanda amma na bogi a hannunsu.

Ya kara da cewa tuni aka tasa keyarsu zuwa Kotu wadda ta tura su Kurkuku na Kirim kiri

DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post